(ABNA24.com) Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa batun Falasdinu da Qudus mai tsarki shi ne batu mafi mahimanci ga Duniyar musulinci kuma tunanin al'ummar musulmi ga makiya ba zai bayar da damar a manta da wadannan wurare masu tsarki ba.
A yayin da yake gudanar da jawabi a gaban mahalarta taron makon hadin kai karo na 33 da ya gudana a nan birnin Tehran a safiyar yau alhamis, shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rouhani ya yi ishara kan rashin cin nasarar makircin makiya wato gwamnatin Amurka da haramtaciyar kasar Isra'ila na dakile farkawar al'ummar musulmi a Duniya, inda ya ce kisan da ake yiwa al'ummar musulmi a kasashen Iraki da Afganistan da Yemen gami da sanya sabani tsananin al'ummar Musulmi da raba kasashen musulinci, shiri ne da makarkashiyar Amurka a yankin.
Rouhani ya tabbatar da cewa wajibi ne Falasdinu ta koma hanun Falastinawa da al'ummar musulmi sannan ya kamata matasa musulmi su san babu yadda za a yi kasar Amurka ta kasance abokiya ga musulmi da yankin, kuma babu wani da zai warware matsala da kuma rikicin da yankin ke fuskanta face al'ummar yankin.
Har ila yau shugaba Rouhani ya nuna bakin cikinsa kan yadda wasu kasashen musulmi ke kulle dangantaka da haramtaciyar kasar Isra'ila har ma suna amfani da na'urorin leken asirinta domin cutar da wasu musulmi, inda ya ce kasar Iran ita ce a sahu na farko wajen tunkarar haramtaciyar kasar Isra'ila da Amurka wajen goyon bayan al'ummar Falastinu.
A yau Alkhamis ne aka bude taro makon hadin kai na kasashen musulmi karo na 33 wanda ya samu halartar manyan malimai daga kasashe daban-daban na Duniya.
/129
16 Nuwamba 2019 - 09:06
Lambar labari: 988315
Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa batun Falasdinu da Qudus mai tsarki shi ne batu mafi mahimanci ga Duniyar musulinci kuma tunanin al'ummar musulmi ga makiya ba zai bayar da damar a manta da wadannan wurare masu tsarki ba.